New Posts

Thursday, November 1, 2018

Inanan Tare Dake Ko Da Daukaka Ko Babu Inji Zango


Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango kenan tare da tauraruwar fim din Hausa da tauraruwar ta ta lafa, Zainab Indomie, Adamu ya bayyana cewa yana tare da ita cikin daukaka da rashinta, cikin arziki da talauci, ya kare da cewa Allah yi miki Albarka Indo.

 A bayadai tauraruwar Zainab ta haskaka sosai a fina-finan Hausa amma sai aka dena jin duriyarta, an yita surutai iri-iri akan abinda ya sa aka daina jin duriyar Zainab ciki hadda wanda aka rika cewa ciwon kanjamaune ya kamata. Amma ta fito ta karyata hakan harma tayi Allah ya isa ga duk wanda suka mata wancan kazafin. A ‘yan kwanakinnan dai Zainab ta fito ta bayyanawa Duniya cewa ta dawo harkar fim.

Wednesday, October 31, 2018

Tsohuwar yar fim mai sun Zainab Indomie ta dawo fim ko me yasa ?


Bayan kusan shekara biyar ba a jin duriyarta a harkar fina-finan Kannywood, Zainab Abdullahi ta yanke shawarar komawa bakin sana'arta. Zainab Indomie, kamar yadda masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai. Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu. Sai dai tana tsakiyar tashe aka daina jin duriyar jarumar, abin da ya kai ga ana diga ayar tambaya da yada jita-jita a kan dalilan daina ganinta a fina-finai. "A lokacin da jarumar ke kan ganiyarta kusan ana iya cewa ta yi wa sauran matan wannan masana'antar fintinkau", a cewar Kabiru Jammaje, wani mai shirya fina-finai a masana'antar Kannywood. Jammaje ya ce akwai daraktoci da masu shirya fina-finan wadanda yanzu haka suka shirya su yi aiki da Indomie saboda hikima da kuma kwarewarta a harkar fina-finai.

 Mece ce hakikanin abin da ya boye Indomie?A ina 'Yan Sanda Suka a Jiye 'YenShi'a 400 Da Suka Kama ?


kasar. Wata sanarwa da kakakin rundunar Mr Jomoh Moshood ya aike wa manema labarai ta kara da cewa an kama mutanen ne dauke da kwalabe 31 na bama-baman da aka hada da fetur da muggan makamai. A cewar sanarwar ana gudanar da bincike kan 'yan Shi'ar kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu. Mr Moshood ya zargi mabiyan Sheikh Ibrahim El-Zakzakky da kona motocin 'yan sanda da tayar da hargitsi inda ya ce babban sufeton 'yan sandan kasar ya ba da umarni ga 'yan sanda su murkushe 'ya'yan kungiyar a dukkan inda suke a fadin Najeriya. "An sanya kwamishinonin 'yan sandan jihohin da akwai mabiya kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta El-Zakzakky da su shiga cikin shirin ko-ta-kwana domin murkushe su kamar yarda doka ta tanada sannan su hana 'yan kungiyar tayar da kayar baya a jihohin," in ji sanarwar. Tun daga karshen makon jiya ne dai mabiya El-Zakzakky suka soma isa Abuja inda za su yi gangami na jimanin mutuwar Hussain, jikan manzon Allah Annabi Muhammad(SAW) wanda ake yi duk shekara. Kalli hotunan artabun 'yan Shi'a da sojoji a Abuja Mun kashe 'yan Shi'a — Sojin Nigeria Sai dai sun yi zargin cewa jami'an tsaro sun hana su shiga lamarin da ya haddasa arangama tsakaninsu har aka yi asarar rayuka. Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta fitar ranar Litinin ta ce an kashe mabiya Shi'a uku yayin da sojoji suka jikkata akamakon taho-mu-gamar da aka yi a tsakaninsu. Sanarwar ta ce 'yan Shi'a sun far wa dakarunta da ke sanya ido a wuraren binciken ababen hawa da ke gadar Kugbo/Karu. "Mabiya mazahabar wadanda ke da matukar yawa sun kutsa kai ta shingen binciken ababen hawa inda suka turmushe 'yan sanda. "Daga nan ne 'yan sandan suka janye inda suka shiga cikin sojojin da ke yunkurin dakile harbe-harben da mutanen ke yi," in ji sanarwar. Ta kara da cewa "lokacin arangamar ne mabiya mazahabar uku suka mutu san nan soji hudu suka jikkata, inda aka tura su asibiti domin karbar magani." Amma 'yan Shi'a sun ce jami'an tsaron Najeriya sun kashe mambobinsu 24


Sunday, October 28, 2018

Duk alkawuran da na dauka na cika maku –Buhari ya fadawa ‘Yan Najeriya
Na cika alkawurorin da na yi wa
mutanen Najeriya – Inji Shugaba
Buhari
Yayin da ake shiryawa zaben 2019,
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
bayyana cewa ya cika alkawarin da ya
dauka na kawo karshen ta’addacin Boko
Haram da magance matsalar tsaro a fadin
kasar.
Shugaba Buhari yace ya shawo kan matsalar
tsaro a Najeriya
A Ranar Juma’a Shugaba Muhammadu
Buhari ya jaddada cewa ya shawo kan
matsalar rashin tsaro a Najeriya duk da
abubuwan da ‘Yan adawa ke fada.
Shugaban kasar yace an ci nasara wajen
yaki da ‘Yan ta’addan Boko Haram.
Shugaban kasar yace ya kuma yi
namijin kokari wajen gyara hanyoyi da
yin tituna da layin dogo a cikin shekaru
3 da yayi a kan kujera.
Buhari yace
mutanen Arewa-maso-Gabas za su bada
labarin irin kokarin da Gwamnatin sa
tayi.
Shugaban kasar Buhari ya kuma yi
wani bayani ta shafin sa na Tuwita
inda yace za su yi kokarin gyara tituna
da kuma manyan hanyoyin dogo na
jirgin kasa yadda za a ratsa kowane
Gari tare da gyara hanyan jiragen sama
na Kasar.
Sai dai duk da cin karfin ‘Yan Boko
Haram da aka yi, sha’anin tsaro ya
tabarbare a Yankin Benuwai, Zamfara,
Filato da kuma Taraba da Kaduna har
ma da wasu kasashen Yarbawa inda su
ka gamu da mugun rikicin Makiyaya.
Shugaban kasar yace su na cigaba da
kokarin gyara harkar wutan lantarki.
Dama dai tun farkon shekarar nan
Gwamnatin Buhari tayi alkawarin cewa
zuwa badi za a ga canji a harkar wutan
lantarki.

Dan Atiku ya bayyana wani muhimmin sirri a kanmahaifinsa -


Dan takarar shugaban kasa a karkashin
jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, na
sadaukar da lokaci domin inganta rayuwar
iyalinsa ta hanyar koyar wa tare da saka
su a cikin harkokin kasuwancinsa da za su
gada, kamar yadda dansa ya bayyana.
Mustapha Atiku Abubakar, da ga Atiku
Abubakar, ne ya sanar da hakan a jiya
juma'a, a shafinsa na Tuwita.
Mustapha ya bayyana yadda ya kasance
cikin irin taron duk shekara da Atiku ke
shiryawa iyalinsa tun yana da shekaru
12 da haihuwa.
Mustapha na wadannan ne a matsayin
raddi ga wani Henry Okelue bayan ya
zargi Atiku da daina neman wani ilimi
a cikin shekaru 49 da su ka wuce.
Atiku
Mustapha ya yi bayanin yadda
mahaifinsa ke ilimintar da kansa da
iyalinsa domin ganin inganta rayuwar
sa da ta iyalinsa tare da kokarin koya
ma su dabarun neman kudi domin
dogaro da kai.
Ina da shekaru 12 lokacin da na fara
raka mahaifina aji domin daukan darasi.
Duk shekara sai mahaifinmu ya gayyato
manyan Farfesoshi domin su ilimantar
da mu.
Tsawon shekaru 10 kenan yanzu
ina halartar irin wannan ajin daukan
darasi da mahaifin mu ya farlanta duk
'ya'yansa halarta," in ji Mustapha.
Daga cikin irin masana da Mustapha ya
lissafa sun taba gabatar da lakca a daya
daga cikin ajin iyalin Atiku akwai
Farfesa Gimeno na kasar Spain da
babban lauyan Najeriya, Eyitayo Jegede.

Shugaba Buhari ya hada mayan Kannywood liyafa a fadarsa


Shugaban ya gayyaci jaruman ne domin nuna
farin cikin sa bisa goyon baya da suke bashi
wajen tafiyar da alamuran kasa tare da kokarin
da suka bayarwa wajen gani ya zarce a zaben
2019.
Manyan jiga-jigan masana'antar fina-finan
da wakokin hausa ta Kannywood sun
ziyarci fadar shugaban kasa domin yin
liyafa da shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaban ya gayyaci jaruman ne domin nuna
farin cikin sa bisa goyon baya da suke bashi
wajen tafiyar da alamuran kasa tare da kokarin
da suka bayarwa wajen gani ya zarce a zaben
2019.
Fadar shugaban dake Abuja ta karbi bakoncin
yan wasan daren ranar Alhamis 18 ga watan
Oktoba 2018.
Tawagar yan wasan da suka halarci liyafar tare
da shugaban sun hada da shugabanni masu rike
da muhimman mukamai a Kannywood tare da
jarumai maza da mata da mawaka tare da
manyan masu shirya fina-finai da masu bada
umarni.
Cikin manyan bakin da suka halarci liyafar da
shugaban ya shirya ma yan wasan sun hada da
gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufai ,
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da dan
majalisar wakilai na tarayya, Honarabul Nasir Ali
Ahmed .
A bangaren ma'aikatan fadar shugaban kasa
akwai shugaban ma'aikatan fadar, Mallam Abba
Kyari , Sakataren gwamnatin tarayya, Boss
Mustapha sai hadimin shugaban a bangaren
yadda labarai na kafafen sada zumunta, Bashir
Ahmad.
Yan kannywood sun » nuna goyon bayan su ga
shugaban na zarcewaa saman kujerar
shugabancin kasa a zaben 2019.
Yayin da yake jawabi wajen liyafar, Nura
Hussein ya jaddada cewa "2019 Ba kudi ba, sai
dai a danna mu a yanke. Zamu dangwala maka da
jinnin mu,".
Fadar shugaban tayi ma yan wasan alkawarin
wajen yaki tare da kawo karshen masu satar
fasaha wanda ke gurgunta alamuran
masana'antar nishadi.
Tun ba yau ba wasu daga cikin fitattun jaruman
suke nuna goyon bayan su ga dan takarar APC a
zaben dake gabatowa.
Wasu daga cikin su sun wallafa hotuna tare da
fitar da wakoki domin tabbatar da matsayin su
ga shugaban gabanin zaben

Saturday, October 27, 2018

Yan mata tagwaye da akasace a zamfara yayin da sukeshirye-shiryen auren su


Barayin sun sace Hassana da Husainan ne a
garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi na
jihar Zamfara a karshen makon da ya shude.
Al'ummar jihar Zamfara na kewa yayin da
wasu barayi suka sace tagwaye wadanda
ake shirye-shiryen bikin auren su.
Masu garkuwan sun sace Hassana da Husainan
ne a garin Dauran dake karamar hukumar Zurmi
na jihar.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, an sace
tagwayen ne tdakanin ranar Asabar da Lahadi
na makon da ya shude.
Mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi,
Abubakar Muhammad , ya shaida ma BBChausa
cewa masu garkuwan sun bukaci a biya su Naira
miliyan 100 kafin su sako tagwayen.
Yace tagwayen suna cikin mutane bakwai daga
karamar hukumar da barayi suka sace kwana-
kwanan nan.
Abubakar yayi kira ga yan Najeriya da su kawo
masu dauki domin kawo karshen matsalar da
suke fuskanta.

Tauraron kannywood, AhmadLawan, ya fitar da kayatattunhotuna na murnar cikashekara goma da aure

Lawan Ahmad ya raya zagayowar wannan muhimmin ranar tare da wallafa wasu
tayatattun hotuna na shi da iyalen sa a shafin
sa na Instagram.
Shahararren jarumin Kannywood, Lawan
Ahmad, bai gaza nuna farin cikin sa na cika
shekaru goma da yin aure kuma dankon
soyayar sa ga iyalen sa na cigaba da yin
kamari.
Jarumin ya raya zagayowar wannan muhimmin
ranar tare da wallafa wasu tayatattun hotuna na
shi da iyalen sa a shafin sa na Instagram.
An gan inda jarumi ya haskaka tare da matar sa
da yaransu uku da suka samu albarkacin auren
su.
Allah ya albarkaci auren su da yara uku, maza
biyu Ahmad Lawan Ahmad, Aliyu Lawan Ahmad
da yar auta, Fatima Lawan Ahmad.
Cikin sakon da ya fitar, jarumin ya nuna godiyar
sa bisa addu'o'i da fatan alheri da ya samu
daga dinbim masoyan sa da sauran abokan
sana'ar sa.
Lawan Ahmad yana daya daga cikin tsofafin
fitatun jarumai dake raya masana'antar fina-
finan hausa kai ga wannan zamani.
Bayan fim, Lawan ya nuna sha'awar sa na shiga
harkar siyasa.
Ya fito takarar majalisar jiha
karkashin jam'iyar APC na wakiltar karamar
hukumar Danja dake jihar Katsina. Sai dai bai
samu nasarar zama gwanin jam'iyar ba.

Monday, October 8, 2018

APC ba ta yi adalci ba a zabukan fitar da gwani — Aisha Buhari


Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta soki jam'iyya mai mulki APC dangane da yadda ta gudanar da zabukan fitar da gwaninta a 2018. Aisha Buhari, wadda ta rubuta a shafinta na Instagram cewa ' Abin takaici ne wasu 'yan takara sun yi amfanin da kudin guminsu sun sayi fom din takara, sannan an tantance su, kana sun yi yakin neman zabe iya karfinsu, amma kuma an cire sunayensu a ranar zabe.' Uwargidan shugaban Najeriyar, ta ce ' Babban abin takaicin shi ne yadda wadannan 'yan takara suka sayi fom din a kan kudi mai yawa'. Ta ce ' Da yawa daga cikin wasu 'yan takarar kuma har yanzu suna dakon sakamakon zaben, wanda sanin kowa ne cewa tuni aka ba wa wasu takarar shi yasa ake jan kafa wajen fadin sakamakon.' Aisha Buhari ta ce, Makasudin kafa jam'iyyar APC shi ne don a samar da sauyi nagari, amma bain takaicin shi ne yadda wannan al'amari ya faru a karkashin jagorancin Adams Oshimole, mutumin da aka sani da nuna damuwa da kuma kokarin kwatowa talakawa 'yancinsu. Uwargidan shugaban Najeriyar ta ce, wannan al"amari ya sa mutum ba shi da zabi illa ya nesantar da kansa daga wannan rashin adalcin ya kuma yi magana a madadin wadanda aka tauye musu hakkinsu. Ta ce yana da muhimmanci al'umma su tashi tsaye wajen ganin cewa ba a tauye musu hakkinsu ba. Sai dai wasu na ganin Aisha Buhari, ta yi wadannan kalamai ne saboda rashin samun tikitin takarar kujerar gwamna a jihar Adamawa a jam'iyyar APC da uwanta ya yi.

APC ta cewa Atiku shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne


Jam'iyya mai mulki a Najeriya APC ta yi wa dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar shaguben cewa, shugabancin kasar ba na sayarwa ba ne. A wata sanarwa da jam'iyyar APC ta fitar ta yi zargin cewa "tsohon shugaban kasar ya yi amfani da kudi ne wajen sayen kuri'un mambobin jam'iyyar don su tsayar da shi takara. "Shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne," in ji APC. APC ta ce "Atiku wanda hamshakin attajiri ne, ya yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u daga wakilan jam'iyyar PDP lokacin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda aka yi ranar Lahadi." Sai dai a wata sanarwa da ita ma jam'iyyar PDP ta fitar ta musanta zargin hakan, inda jam'iyyar ta ce "zarge-zargen marasa tushe ba za su taimaki Shugaba Buhari ba." "Babu kamshin gaskiya a zargin da jam'iyyar APC ta yi cewa wadansu masu neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar PDP sun yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u lokacin zaben fitar da gwani," in ji sanarwar da ta fito daga PDP. Jam'iyyar ta APC ta kuma taya Atiku Abubakar Murnar samun nasarar zaben fitar da gwanin da PDP ta yi a jihar Rivers. A ranar Lahadi ne jam'iyyar PDP ta tsayar da tshon mataimakin shugaban kasar bayan ya samu nasara da kuri'u 1532. An dai gudanar da zaben ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers inda wakilai sama da 3,200 daga jihohin Najeriya 36 da Abuja suka hallara domin zabar dan takarar da zai yi gogayya da hugaba Muhammadu Buhari. Sauran 'yan takarar da suka nemi kejarar shugabancin Najeriyar a jam'iyyar PDP, sun hadar da: Jonah Jang da ya samu kuri'u 19 Datti Baba ya samu kuri'u 5 David Mark ya samu kuri'u 35 Turaki Taminu ya samu kuri'u 65 Sule Lamido ya samu kuri'u 96 Bafarawa ya samu kuri'u 48 Hassan Dankwabo ya samu kuri'u 111 Ahmed Markafi ya samu kuri'u 74 Rabi'u Kwankwaso ya samu kuri'u 158 Olubukola Saraki ya samu kuri'u 317 Aminu Tambuwal ya samu kuri'u 693