Sunday, September 30, 2018

Yanzu-yanzu: Kungiyar Kwadago ta dakatad da yajin aiki, kowa ya koma aiki


Kungiyar kwadagon Najeriya ta dakatad da yajin aikin fadin tarayya da ta fara ranan Laraba, 26 ga watan Satumba, 2018. Shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba, ya sanar da hakan ne a hira da manema labarai yau Lahadi, 30 ga watan Satumba a birnin tarayya Abuja. Yace: "An dakatad da yajin aikin daga yau Lahadi," Wannan dakatarwan yana nufin cewa dukkan ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki ranan Talata tun da gwamnatin tarayya ta bayar da ranan Litinin hutun zagayowan yancin kan Najeriya. Ma'aikatan sun bukaci gwamnatin tarayya ta kara musu albashi mafi karancin zuwa N50,000 sabanin N18,000 da ake biya yanzu. Hadaddiyar kungiyar kwadago daya kunshi NLC da TUC sun bayyana cewa zasu rufe duk wasu filayen sauka da tashin jirage dake Najeriya don tabbatar da duk ma’aikata sun bi umarnin kungiyar na shiga yajin aikin dindindin a Najeriya. Majiyar DANHAUSA.tk ta ruwaito shugaban kungiyar kwadago na jahar Legas, Amechi Asugwuni ne ya tabbatar da wannan umarni na uwar kungiyar kwadago ta kasa a wata tattaunawa da yayi da yan jaridu a ranar Alhamis 27 ga watan Satumba a garin Legas.


EmoticonEmoticon