Monday, October 8, 2018

APC ta cewa Atiku shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne


Jam'iyya mai mulki a Najeriya APC ta yi wa dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP Atiku Abubakar shaguben cewa, shugabancin kasar ba na sayarwa ba ne. A wata sanarwa da jam'iyyar APC ta fitar ta yi zargin cewa "tsohon shugaban kasar ya yi amfani da kudi ne wajen sayen kuri'un mambobin jam'iyyar don su tsayar da shi takara. "Shugabancin Najeriya ba na sayarwa ba ne," in ji APC. APC ta ce "Atiku wanda hamshakin attajiri ne, ya yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u daga wakilan jam'iyyar PDP lokacin zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP wanda aka yi ranar Lahadi." Sai dai a wata sanarwa da ita ma jam'iyyar PDP ta fitar ta musanta zargin hakan, inda jam'iyyar ta ce "zarge-zargen marasa tushe ba za su taimaki Shugaba Buhari ba." "Babu kamshin gaskiya a zargin da jam'iyyar APC ta yi cewa wadansu masu neman takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar PDP sun yi amfani da kudi wajen sayen kuri'u lokacin zaben fitar da gwani," in ji sanarwar da ta fito daga PDP. Jam'iyyar ta APC ta kuma taya Atiku Abubakar Murnar samun nasarar zaben fitar da gwanin da PDP ta yi a jihar Rivers. A ranar Lahadi ne jam'iyyar PDP ta tsayar da tshon mataimakin shugaban kasar bayan ya samu nasara da kuri'u 1532. An dai gudanar da zaben ne a Fatakwal, babban birnin jihar Rivers inda wakilai sama da 3,200 daga jihohin Najeriya 36 da Abuja suka hallara domin zabar dan takarar da zai yi gogayya da hugaba Muhammadu Buhari. Sauran 'yan takarar da suka nemi kejarar shugabancin Najeriyar a jam'iyyar PDP, sun hadar da: Jonah Jang da ya samu kuri'u 19 Datti Baba ya samu kuri'u 5 David Mark ya samu kuri'u 35 Turaki Taminu ya samu kuri'u 65 Sule Lamido ya samu kuri'u 96 Bafarawa ya samu kuri'u 48 Hassan Dankwabo ya samu kuri'u 111 Ahmed Markafi ya samu kuri'u 74 Rabi'u Kwankwaso ya samu kuri'u 158 Olubukola Saraki ya samu kuri'u 317 Aminu Tambuwal ya samu kuri'u 693


EmoticonEmoticon