Sunday, October 28, 2018

Dan Atiku ya bayyana wani muhimmin sirri a kanmahaifinsa -


Dan takarar shugaban kasa a karkashin
jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, na
sadaukar da lokaci domin inganta rayuwar
iyalinsa ta hanyar koyar wa tare da saka
su a cikin harkokin kasuwancinsa da za su
gada, kamar yadda dansa ya bayyana.
Mustapha Atiku Abubakar, da ga Atiku
Abubakar, ne ya sanar da hakan a jiya
juma'a, a shafinsa na Tuwita.
Mustapha ya bayyana yadda ya kasance
cikin irin taron duk shekara da Atiku ke
shiryawa iyalinsa tun yana da shekaru
12 da haihuwa.
Mustapha na wadannan ne a matsayin
raddi ga wani Henry Okelue bayan ya
zargi Atiku da daina neman wani ilimi
a cikin shekaru 49 da su ka wuce.
Atiku
Mustapha ya yi bayanin yadda
mahaifinsa ke ilimintar da kansa da
iyalinsa domin ganin inganta rayuwar
sa da ta iyalinsa tare da kokarin koya
ma su dabarun neman kudi domin
dogaro da kai.
Ina da shekaru 12 lokacin da na fara
raka mahaifina aji domin daukan darasi.
Duk shekara sai mahaifinmu ya gayyato
manyan Farfesoshi domin su ilimantar
da mu.
Tsawon shekaru 10 kenan yanzu
ina halartar irin wannan ajin daukan
darasi da mahaifin mu ya farlanta duk
'ya'yansa halarta," in ji Mustapha.
Daga cikin irin masana da Mustapha ya
lissafa sun taba gabatar da lakca a daya
daga cikin ajin iyalin Atiku akwai
Farfesa Gimeno na kasar Spain da
babban lauyan Najeriya, Eyitayo Jegede.


EmoticonEmoticon