Sunday, October 28, 2018

Duk alkawuran da na dauka na cika maku –Buhari ya fadawa ‘Yan Najeriya
Na cika alkawurorin da na yi wa
mutanen Najeriya – Inji Shugaba
Buhari
Yayin da ake shiryawa zaben 2019,
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya
bayyana cewa ya cika alkawarin da ya
dauka na kawo karshen ta’addacin Boko
Haram da magance matsalar tsaro a fadin
kasar.
Shugaba Buhari yace ya shawo kan matsalar
tsaro a Najeriya
A Ranar Juma’a Shugaba Muhammadu
Buhari ya jaddada cewa ya shawo kan
matsalar rashin tsaro a Najeriya duk da
abubuwan da ‘Yan adawa ke fada.
Shugaban kasar yace an ci nasara wajen
yaki da ‘Yan ta’addan Boko Haram.
Shugaban kasar yace ya kuma yi
namijin kokari wajen gyara hanyoyi da
yin tituna da layin dogo a cikin shekaru
3 da yayi a kan kujera.
Buhari yace
mutanen Arewa-maso-Gabas za su bada
labarin irin kokarin da Gwamnatin sa
tayi.
Shugaban kasar Buhari ya kuma yi
wani bayani ta shafin sa na Tuwita
inda yace za su yi kokarin gyara tituna
da kuma manyan hanyoyin dogo na
jirgin kasa yadda za a ratsa kowane
Gari tare da gyara hanyan jiragen sama
na Kasar.
Sai dai duk da cin karfin ‘Yan Boko
Haram da aka yi, sha’anin tsaro ya
tabarbare a Yankin Benuwai, Zamfara,
Filato da kuma Taraba da Kaduna har
ma da wasu kasashen Yarbawa inda su
ka gamu da mugun rikicin Makiyaya.
Shugaban kasar yace su na cigaba da
kokarin gyara harkar wutan lantarki.
Dama dai tun farkon shekarar nan
Gwamnatin Buhari tayi alkawarin cewa
zuwa badi za a ga canji a harkar wutan
lantarki.


EmoticonEmoticon