Sunday, October 28, 2018

Shugaba Buhari ya hada mayan Kannywood liyafa a fadarsa


Shugaban ya gayyaci jaruman ne domin nuna
farin cikin sa bisa goyon baya da suke bashi
wajen tafiyar da alamuran kasa tare da kokarin
da suka bayarwa wajen gani ya zarce a zaben
2019.
Manyan jiga-jigan masana'antar fina-finan
da wakokin hausa ta Kannywood sun
ziyarci fadar shugaban kasa domin yin
liyafa da shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaban ya gayyaci jaruman ne domin nuna
farin cikin sa bisa goyon baya da suke bashi
wajen tafiyar da alamuran kasa tare da kokarin
da suka bayarwa wajen gani ya zarce a zaben
2019.
Fadar shugaban dake Abuja ta karbi bakoncin
yan wasan daren ranar Alhamis 18 ga watan
Oktoba 2018.
Tawagar yan wasan da suka halarci liyafar tare
da shugaban sun hada da shugabanni masu rike
da muhimman mukamai a Kannywood tare da
jarumai maza da mata da mawaka tare da
manyan masu shirya fina-finai da masu bada
umarni.
Cikin manyan bakin da suka halarci liyafar da
shugaban ya shirya ma yan wasan sun hada da
gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufai ,
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da dan
majalisar wakilai na tarayya, Honarabul Nasir Ali
Ahmed .
A bangaren ma'aikatan fadar shugaban kasa
akwai shugaban ma'aikatan fadar, Mallam Abba
Kyari , Sakataren gwamnatin tarayya, Boss
Mustapha sai hadimin shugaban a bangaren
yadda labarai na kafafen sada zumunta, Bashir
Ahmad.
Yan kannywood sun » nuna goyon bayan su ga
shugaban na zarcewaa saman kujerar
shugabancin kasa a zaben 2019.
Yayin da yake jawabi wajen liyafar, Nura
Hussein ya jaddada cewa "2019 Ba kudi ba, sai
dai a danna mu a yanke. Zamu dangwala maka da
jinnin mu,".
Fadar shugaban tayi ma yan wasan alkawarin
wajen yaki tare da kawo karshen masu satar
fasaha wanda ke gurgunta alamuran
masana'antar nishadi.
Tun ba yau ba wasu daga cikin fitattun jaruman
suke nuna goyon bayan su ga dan takarar APC a
zaben dake gabatowa.
Wasu daga cikin su sun wallafa hotuna tare da
fitar da wakoki domin tabbatar da matsayin su
ga shugaban gabanin zaben


EmoticonEmoticon