Wednesday, October 31, 2018

Tsohuwar yar fim mai sun Zainab Indomie ta dawo fim ko me yasa ?


Bayan kusan shekara biyar ba a jin duriyarta a harkar fina-finan Kannywood, Zainab Abdullahi ta yanke shawarar komawa bakin sana'arta. Zainab Indomie, kamar yadda masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai. Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu. Sai dai tana tsakiyar tashe aka daina jin duriyar jarumar, abin da ya kai ga ana diga ayar tambaya da yada jita-jita a kan dalilan daina ganinta a fina-finai. "A lokacin da jarumar ke kan ganiyarta kusan ana iya cewa ta yi wa sauran matan wannan masana'antar fintinkau", a cewar Kabiru Jammaje, wani mai shirya fina-finai a masana'antar Kannywood. Jammaje ya ce akwai daraktoci da masu shirya fina-finan wadanda yanzu haka suka shirya su yi aiki da Indomie saboda hikima da kuma kwarewarta a harkar fina-finai.

 Mece ce hakikanin abin da ya boye Indomie?
EmoticonEmoticon